Kusan mutane 40 ne suka bace bayan da wani kwale-kwalen yan cirani ya kife

0 348

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutane 40 ne suka bace bayan da wani kwale-kwalen yan cirani ya kife a tsibirin Lampedusa na kasar Italiya.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne jirgin ya yi hatsari kuma akalla jariri daya da aka haifa yana cikin wadanda suka bata, in ji wakilin Chiara Cardoletti.

Jirgin ruwan ya taso ne daga birnin Sfax na kasar Tunisia kuma yana dauke da bakin haure 46 daga kasashen Kamaru, Burkina Faso da Ivory Coast, a cewar kakakin hukumar kula da shige da fice ta Majalisar Dinkin Duniya.

Tsibirin Lampedusa na kudancin Italiya na daya daga cikin wuraren da bakin haure ke bi ta tekun Bahar Rum. Ko a bara, fiye da mutane dubu 46 ne suka isa wajen, daga cikin jimillar mutane dubu 105 a Italiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: