Kungiyoyin ma’aikatan jami’a sun umurci mambobinsu da su fito zanga-zanga ranar Talata

0 193

Kungiyar ma’aikatan jami’a ta NASU da kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’I (SSANU) sun umurci mambobinsu da ke fadin kasa da su fito zanga-zanga a fadin kasar. Hakan ya biyo bayan karshen tattaunawar da aka yi tsakanin Ministocin Ilimi da Kwadago, da kwamitin hadin gwiwa na bangarorin biyu. A wata takardar da aka bayar ga daukacin shugabannin rassan kungiyoyin biyu da aka rabawa wa manema labarai a Abuja, kungiyoyin sun ce za a fara zanga-zangar ne a gobe Talata, 9 ga watan Yuli a sassan jihohi, da kuma wata zanga-zanga ta kasa a Abuja ranar 18 ga watan Yuli. . Sanarwar ta samu sa hannun babban sakataren kungiyar ta NASU kuma shugaban SSANU na kasa Prince Peters Adeyemi da kuma Kwamared Mohammed H. Ibrahim.

Leave a Reply

%d bloggers like this: