Kungiyoyin lafiya sun yi Allah-wadai da matakin hana kwararrun likitoci zuwa hutu kasashen waje

0 212

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta kasa da hadin gwiwar kungiyoyin lafiya sun yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na hana wa kwararrun likitocin kiwon lafiya hutu zuwa kasashen waje.

Kungiyoyin na lafiya sun ce kamata ya yi Gwamnatin Tarayya ta magance matsalolin da ke sa ma’aikatan lafiya yin hijira zuwa kasashen waje domin neman wuraren ayukka.

Karamin Ministan Lafiya, Dokta Tunji Alausa, a ranar Asabar din da ta gabata ya bayyana cewa gwamnati ta bayar da umarnin cewa ma’aikatan kiwon lafiya da za su je kasashen waje domin neman rayuwa mai inganci dole ne su yi murabus daga mukamansu kafin su fara irin wannan tafiye-tafiye. Alausa ya ce lokaci ya wuce da ma’aikatan kiwon lafiya ke tafiya zuwa wasu kasashe don neman ingantacciyar rayuwa bayan neman hutu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: