kungiyoyin kwadago zasu jira hakuncin shugaban kasa kan mafi karancin albashin da kwamatin ta kayyade:NLC

0 166

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC Joe Ajaero yace gamayyar kungiyoyin kwadago zasu jira hakuncin shugaban kasa Bola Tinubu kan daftarin shawarwari, kan mafi karancin albashi da kwamatin ta kayyade.

Ajaero yace ba zasu dauki kowane mataki ba har sai shugaban kasa ya bayyana matsayinsa kan shawarwari biyu da aka gabatar masa na sabon mafi karancin albashin ma’aikata a kasa.

Yayin da kungiyar kwadago ta dage kan biyan Naira dubu 250 a matsayin albashin ma’aikata, sai kuma bangaren gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kamfanoni masu zaman kansu da suka amince da kudirin Naira dubu 62.

Kwamitin ya mika shawarwarin biyu ga shugaban kasa a jiya, ta hannun sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

Sa’o’i kadan bayan mika rahotan da ke kunshe da shawarwari guda biyu ga Shugaban kasa, Ajaero ya ce sassan NLC da na TUC za su yanke hukunci kan mataki na gaba, bayan Shugaban kasa ya amince da duk shawarwari biyun.

Kungiyar ta ce wa’adin mako guda da aka baiwa gwamnatin tarayya a ranar Talatar da ta gabata, zai kare ne da tsakar daren yau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: