Kungiyar Kwadago ta kasa, NLC, da Kungiyar ‘Yan Kasuwa ta TUC sun yi tir da ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas tare da dakatar da zababbun shugabannin jihar da shugaba Tinubu ya yi.
Kungiyoyin sun bayyana matakin Shugaban kasar a matsayin take doka, suna masu cewa hakan ya saba wa Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin kasar na 1999.
Sun bukaci a janye wannan mataki nan take domin kare dimokuradiyya da kwanciyar hankalin ma’aikata da tattalin arzikin kasar nan.
A wata sanarwa kan wannan batu da shugabannin NLC da TUC suka fitar, sun gargadi gwamnati da kada ta mayar da Najeriya kasar da ake wulakanta dokokin mulkin dimokuradiyya.