Kungiyoyin Kwadago da Gwamnatin Tarayya sun samu sabani kan gazawar biyan albashin ma’aikata

0 274

Kungiyoyin Kwadago da Gwamnatin Tarayya sun samu sabani kan gazawar biyan albashin ma’aikata na Naira dubu 35.

Ma’aikatan gwamnatin tarayya, a wata tattaunawa daban-daban da suka yi da manema labarai a jiya litinin, sun bayyana cewa gwamnatin tarayya ta biya albashin Naira dubu 35 ne kawai a watan Satumba 2023.

Bayan cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi   bayan hawan sa mulki, gwamnatin tarayya ta amince ta biyan kowane ma’aikacinta naira dubu 35 domin rage radadin cire tallafin man fetur. Gwamnatin, a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Shugaban Hukumar Kula da Albashin Ma’aikata ta Kasa, Ekpo Nta, ta bayyana cewa biyan albashin ma’aikata zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: