kungiyoyin da ke son barin gasar zakarun Turai, Italiya za ta hukunta su

0 214

An kirkiri wasu sabbin dokokin da suka hana kowanne kwallon kafa ta cikin gida a Italiya.

Hukumar kwallon kafa ta kasar Italiya ta sabunta dokokin hukunta duk kungiyar da ke nuna sha’awar ballewa daga gasar zakarun nahiyar Turai zuwa sabuwar gasar da wasu kungiyoyi ke shirin girkawa ta European Super League.

Kungiyoyin Juventus da AC Milan da ke cikin gasar Serie A, na cikin kungiyoyin da ke shirin ballewa a Italiya zuwa sabuwar gasar European Super League.

Sauran kungiyoyin sun hada da wasu manyan kungiyoyin da ke a Ingila kamar Arsenal da Chelsea da Liverpool da Manchester City da Manchester United da kuma Tottenham, sai Atletico Madrid da Bercelona da Real Madrid a kasar Spain.

Leave a Reply

%d bloggers like this: