Kungiyar RIPAN Tayi Kira Ga Tinubu Da Ya Cigaba Da Tsare-Tsaren Samar Da Abinci Domin Bunkasar Tattalin Arziki
Kungiyar masu sarrafa shinkafa ta kasa, RIPAN, ta yi kira ga zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya ci gaba da tsare-tsaren samar da abinci domin bunkasar tattalin arziki.
Darakta Janar na kungiyar Andy Ekwelem ne ya yi wannan kiran yau a Abuja a wani taron manema labarai.
A cewar Andy Ekwelem, RIPAN kungiya ce ta masu saka hannun jari a harkar sarrafa shinkafa, wacce aka kafa a matsayin martani kai tsaye ga shirin gwamnatin tarayya na bunkasa noman shinkafar gida.
Ya ce ayyukan nomawa da sarrafa shinkafar da ’ya’yan kungiyar ke yi na bayar da gudunmawar samar da dubban ayyukan yi kai tsaye da kuma miliyoyin wasu ayyukan ga masu ruwa da tsaki a harkar shinkafa da sauran bangarori masu alaka da shinkafa.
Ya ce masana’antar shinkafa ita ce ta farko wajen daukar ma’aikata mafi mafiya yawa a Najeriya, inda ta samar da ayyukan yi ga sama da mutane miliyan 13.
A cewarsa, harkar noman shinkafa a Najeriya ta samu gagarumin tallafi daga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.