Kungiyar NUJ ta shawarci gwamnatin tarayya da ta kawo karshen matsalar karancin man fetur

0 208

Kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ, reshen jihar Oyo ta shawarci gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ta samar da mafita mai dorewa kan matsalar karancin man fetur da ke kara kamari a kasar.

Kungiyar ta bayar da shawarar ne a a jiya  Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa ana sayar da litar man fetur tsakanin Naira 700 zuwa 820 a sassan Ibadan, a jiya Litinin.

Kungiyar ta yan jarida a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Kwamared Ademola Babalola, wadda aka aikewa manema labarai ta hannun sakataren kungiyar Kwamred Olusola Oladapo, ta shawarci shugaban kasar da ya magance matsalolin cikin gaggawa.

Sanarwar ta kara da cewa ‘yan Najeriya da dama na fuskantar kunci sakamakon karancin man fetur a kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: