Kungiyar NATCA ta gargadi gwamnati kan karancin ma’aikatan kula da zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya
Kungiyar masu kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya, NATCA, ta gargadi gwamnati kan karancin ma’aikatan kula da zirga-zirgar jiragen sama a kasar, tana mai bukatar daukar sabbin ma’aikata da horar da su.
Shugaban kungiyar, Amos Edino, ya bayyana cewa karancin ma’aikata yana jefa jami’ai cikin gajiya da matsin lamba, domin suna aiki fiye da lokacin da aka tanada.
Ya ce dalibai a Makarantar Koyar da Harkokin Jiragen Sama ta NCAT da ke Zariya na fama da kalubalen rashin wadatattun kayan koyarwa, yayin da rashin gyaran kayan aiki ke barazana ga tsaro.
Edino ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta sabunta tsarin albashi, ta kuma dauki matakan inganta yanayin aiki da kiwon lafiyar jami’an kula da zirga-zirgar jiragen sama domin tabbatar da ingantaccen tsarin zirga-zirga a kasar.