Kungiyar manoma ta AFAN ta yabawa Gwamna Mallam Umar Namadi

0 324

Hadaddiyar kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Jigawa AFAN ta yabawa Gwamna Mallam Umar Namadi bisa kokarinsa na bunkasa aikin noma a jihar nan.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren kungiyar na jiha Alhaji Yahuza M Isah Birnin Kudu ya aiko dakinmu na labarai

Yace kasancewar bangaren aikin noma na daya daga cikin kudirorin 12 gwamna Umar Namadi, gwamnan ya yi rangwamen takin zamani da bada motocin tan-tan ga kananan hukumomi domin amfanin manoma da kuma bada tallafi wajen bunkasa noman alkama a jihar nan.

Alhaji Yahuza Isa Birni Kudu ya kuma ce gwamnan ya bada umarnin yiwa manoman shinkafa rijista domin kara samun tallafi Sakataren na AFAN na jihar Jigawa ya kuma aike da sakon  taya murna na shigowar sabuwar shekarar miladiyya ta 2024 ga gwamna Umar Namadi da sauran manoman jihar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: