Kungiyar Malaman Jami’oi ta Kasa reshen Jami’ar Gwamnatin Jihar Yobe, ta fara gudanar da yajin aikin gargadi na Makonni 2
Kungiyar Malaman Jami’oi ta Kasa reshen Jami’ar Gwamnatin Jihar Yobe, ta fara gudanar da yajin aikin gargadi na Makonni 2, biyo bayan gazawar gwamnatin jihar wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma tsakanin Kungiyar da kuma Gwamnatin Jihar.
Yajin aikin na zuwa ne bayan da Daliban Makarantar suka kammala rubuta Jarabawar Zangon karatu na 2.
Manema labarai sun gano cewa yajin aikin zai shafi Daliban da suke Ajin karshe, kuma suke rubuta Project.
Shugaban Kungiyar na Jami’ar Barrister Muhammed Saje Jajere, shine ya tabbatar da hakan, inda ya ce wakilan kungiyar ASUU na Kasa sun ziyarci Jihar domin ganin yadda zasu shawo kan Matsalar yajin aikin.
A cewarsa, gwamnatin Jihar ta shirya gudanar da zaman Sulhu tsakanin ta da Mambobin Kungiyar domin samun mafita.
Idan za’a iya tunawa de a ranar 25 ga watan Mayu ne Kungiyar ta fitar da wata sanarwa, mai dauke da Sahannun Shugaban ta, inda take bukatar Shugaban Jami’ar ya shiga Lamarin.
Kazalika, ya yi Alkawarin fadawa manema labarai abinda aka cimma a tattaunawar tasu.