Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta bai wa gwamnatin Kano wa’adin kwanaki 15 da ta gaggauta biya musu bukatunsu
Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) reshen jihar Kano, ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 15 da ta gaggauta biya musu bukatunsu ko kuma ta tsunduma yajin aikin a fadin jihar.
Yanke wa’adin na cikin wata wasika mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren kungiyar kuma jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Kwamared Ahmad Hazmat Sharada, ya biyo bayan wasu bukatu da ba a warware ba tsakanin ma’aikatan jinya da gwamnatin jihar tun daga watan Disambar 2023.
A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 2 ga watan Oktoba kuma aka aika wa shugaban ma’aikatan jihar Kano, NANNM, ta yi gargadin cewa, ma’aikatan jinya da ungozoma a fadin jihar za su janye ayyukansu daga dukkan cibiyoyin kiwon lafiya da cibiyoyin horo idan gwamnati ta gaza biya musu bukatunsu.
Idan har yajin aikin ya tabbata, zai iya haifar da mummunan sakamako ga tsarin kiwon lafiya na jihar saboda janye ayyukan jinya na iya haifar da dakatar da ayyuka masu mahimmanci na asibiti, lamarin da zai shafi marasa lafiya da dama a fadin jihar Kano.
Har yanzu gwamnatin jihar Kano ba ta mayar da martani kan wa’adin da hukumar ta yi ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.