Kungiyar likitocin masu neman kwarewa ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a yau 9 ga watan Agusta 2023.
Shugaban kungiyar, Innocent Orji, ya bayyana hakan a cikin shirin karin kumallo na gidan Channels TV.
A cewarsa, yajin aiki na kungiyar, duk da haka, yana ci gaba.
Shugaban ya ce abokan aikinsa na da manyan bukatu guda takwas da suka hada da bukatar gwamnati ta dauki sabbin ma’aikata domin maye gurbin wadanda suka bar tsarin aikin ta hanyar tafiya kasashen ketare.
Orji ya ce gwamnati ba ta nuna himma wajen biyan bukatun kungiyar ba. Dakatar da zanga-zangar da aka shirya yi ya biyo bayan wata ganawa da shugabannin kungiyar suka yi da majalisar dattawa karkashin jagorancin shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio.