Kafin gudanar da taron gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadagon da aka shirya gudanarwa a yau (Litinin), kungiyar kwadago ta kasa ta ce dole ne gwamnati ta biya bukatunta domin dakile illar cire tallafin man fetur.
Kungiyar ta yi barazanar cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin kira ga ma’aikata da su yi aiki a masana’antu, inda ta ce ta dakatar da yajin aikin da ta ke shirin yi.
Ta bayyana cewa tsadar man fetur na janyo wa ‘yan Najeriya wahalhalun da ba za su iya jurewa ba, inda ta kara da cewa dole ne gwamnati ta yi gaggawar samar da agajin jin kai, kamar yadda kungiyar NLC ta ce tana sa ran karin mafi karancin albashi daga N30,000 zuwa N200,000.
Gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago sun gana a ranar 5 ga watan Yuni, 2023, tare da kudurin sake zama a yau litinin domin cimma matsaya kan tsarin aiwatar da kudurorin da aka cimma.
Tsohon kakakin majalisar wakilai kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, wanda ya jagoranci bangaren gwamnati ne ya bayyana hakan a karshen taron da wakilan kungiyoyin kwadago suka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Daga nan sai ta bukaci shugaba kasa Bola Tinubu da ya tabbatar da cewa an sake bude kan iyakokin kasar domin tabbatar da shigo da abinci da kayan gona cikin sauki.
Ma’ajin kungiyar NLC, Hakeem Ambali ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Abuja.