Kungiyar Kwadago tace za ta matsa lamba kan aiwatar da sabon mafi karancin albashi

0 233

Kungiyar Kwadago ta kasa tace za ta matsa lamba wa gwamnoni da shugabannin kananan hukumomin da suka kasa aiwatar da sabon mafi karancin albashi.

Ma’ajin kungiyar kwadagon Hakeem Ambali, wanda ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a Abuja, ya ce gwamnonin jihohi da dama sun ki biyan mafi karancin albashin ma’aikata a halin yanzu, wanda yace hakan ya ya biyo bayan rashin daukar matakin hukunci da dokar mafi karancin albashi ta shekarar 2019 ta tanada.

Ya bayyana haka ne yayin da manema labarai suka tattaro cewa kwamitin mai mambobi 37 da gwamnatin tarayya ta kafa zai gana a cikin makon nan domin tattaunawa kan rahotannin da wasu kananan kwamitoci daga shiyyoyi shida na kasar nan suka gabatar. A ranar 30 ga watan Junairu, 2024 ne shugaban kasa Bola Tinubu ta bakin mataimakinsa Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin mai mutane 37 kan sabon mafi karancin albashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: