Biyo bayan dakatar da yunkurin tsunduma yajin aikin gama gari a fadin kasa da kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Jigawa, ta fara tattaunawa da gwamnarin jihar Jigawa kan bukatunsu, wanda suka kunshi bayar da tallafin karin mafi karancin albashi na watanni 6.
Shugaban kungiyar na jihar Kwamaret Sunusi Alhassan Maigatari ya bayyana haka ga manema labarai a yunkurin da suke na sasantawa da gwamnatin jihar.
Yayi bayanin cewa, jajircewar da gwamnatin jihar jigawa ta nuna a teburin sasanton, ya basu kwarin guiwa da fatan cimma kyakkyawan sakamakon da zai bunkasa walwalar ma’aikatan jihar.
Yace bukatun nasu sun kunshi bayar da bashi marar ruwa da samar da kayayyakin rage radadi ga ma’aikata. Shugaban kungiyar ya kara da cewa, ma’aikata na cikin mawuyacin hali sakamakon cire tallafin man fetur, wanda ya haifar da tsadar rayuwa da tashin gouron zabin farashin kayayyakin masarufi da sama da kashi 50 cikin 100 da rashin wadataccen albashi.