Kungiyar Kwadago na neman a biya ma’aikatan gwamnati Naira Miliyan daya a matsayin sabon mafi karancin albashi, in ji shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Kwamared Joe Ajaero.
Ajaero ya bayar da hujjar wannan matsayar ne saboda hauhawar farashin kayayyaki da kuma wahalhalun da ma’aikatan ke fuskanta a baya-bayan nan sakamakon cire tallafin man fetur.
Idan an amince da kudurin, ana sa ran za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin a watan Afrilun 2024.
Tuni dai gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin da zai duba mafi karancin albashi daga Naira dubu 30 da ake biya a duk wata. Amma, Ajaero, wanda ya yi magana a gidan talabijin na Arise a jiya Litinin, ya ce sabuwar bukatar ita ma ta biyo bayan tsadar rayuwa ne a karkashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu, wacce ta aiwatar da tsare-tsaren da suka haddasa hauhawar farashin kayayyaki kamar cire tallafin man fetur.