Kungiyar Kwadago ta koka kan karin kudin wutar lantarki ga kwastomomi a rukunin Band A

0 187

A jiya Laraba, Kungiyar Kwadago ta kasa NLC da takwararta ta TUC, sun koka kan karin kudin wutar lantarki ga kwastomomi a rukunin Band A.

Biyo bayan faduwar darajar Naira, da hauhawar farashin kayayyaki, da dai sauransu, hukumar kula da wutar lantarki ta kasa ta sake kara kudin wutar ga kwastomomin kamfanin na rukunin Band A.

Ajiya Laraba, wasu kamfanonin rarraba wutar lantarki da suka hada da na Ibadan, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Eko, da na Kaduna, da dai sauransu, sun sanar da karin farashin Band A daga N206.80 a kowace kilowatt zuwa N209.50 a kowace kilowatt.

ƙungiyoyin ma’aikata,da kamfanoni masu zaman kansu sun yi Allah wadai da karin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: