Kungiyar Kiristoci CAN tayi tir da kisan da wasu masu tsattsauran ra’ayin suka yi wa wani Musulmi a Sakkwato

0 366

Kungiyar Kiristocin ta Kasa CAN ta fitar da wata sanarwa a jiya, inda take tir da kisan da wasu masu tsattsauran ra’ayin suka yi wa wani Musulmi a Sakkwato mai suna Usman Buda.

A cikin sanarwar Shugaban Kungiyar ta CAN Daniel Okoh ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da kare kowane irin dan kasa ba tare da la’akari da addinin da yake ba.

Ƙungiyar Kiristocin ta kuma bukaci jami’an tsaro su kama waɗanda suka kashe mutumin, domin hakan ya zama izina, sannan kuma a kare aukuwar irin hakan anan gaba.

Shi dai marigayi Usman Buda wanda mahauci ne a cikin garin Sokoto, ya rasa ransa ne sakamakon musayar ra’ayi da fahimta da ta shafi addini, inda wasu da ba su fahimce shi ba suka ce ya yi ridda daga karshe suka kashe shi.

Ƴan sanda sun ce sun samu kiran gaggawa yayin da lamarin ya faru, inda suka kai dauki marigayin zuwa asibiti. Bayan sun dauki Usman Buda zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto aka tabbatar masu da cewa ya rasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: