Kungiyar kare hakkin dan adam tayi Allah wadai da harin jirgin maras matuki a Kauyen Tudun Biri

0 219

Kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa da kasa, tayi Allah wadai da harin jirgin maras matuki na sojojin kasar nan da aka kaiwa masu bikin Maulidi a Kauyen Tudun Biri na Jihar Kaduna, wanda halaka mutane sama da 80.

Darakatan Kungiyar a Najeriya Amb Abdullahi Adamu-Bakoji cikin wata sanarwa da ya fitar a makon da ya gabata, ya nuna damuwa cewa daga shekarar 2014 zuwa 2023 sama da mutane 300 harin sojojin kasar bisa kuskure ya halaka.

A cewar sa,wadannnan kashe-kashe sunyi yawa a yi la’akari da su a matsayin kuskure.

Yace, irin harin na faruwa kusan duk shekara amma gwamnati bata dauki wani mataki domin kare afkuwar sa, ko kare rayukan mutane ba. Daraktan Kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa na Najeriya, yayi gargin cewa duniya na kallon lamarin zai cigaba da faruwa da batare da an dauki mataki ba, ko yaya?

Leave a Reply

%d bloggers like this: