Kungiyar Kananan Hukumomin kasar nan ta nuna damuwa kan shirin biyan mafi karancin albashi na N62,000, inda ta dage cewa idan har aka amince da biyan albashin na iya kawo cikas da kuma haifar da matsalolin kudi ga kananan hukumomi.
Manema labarai sun ruwaito cewa gwamnatin tarayya a ranar Larabar da ta gabata ta gargadi kungiyar kwadagon da ta yi la’akari da babban tasirin tattalin arzikin biyo bayan neman karin mafi karancin albashi na kasa.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, wanda ya bayyana hakan yace Karin albashin da kungiyar kwadagon ke nema zai iya gurgunta tattalin arzikin kasa, ya kuma haifar da korar ma’aikata da yawa tare da kawo cikas ga jin dadin ‘yan Najeriya.
Sai dai kungiyoyin kwadago sun musanta ikirarin shugaban kasa Bola Tinubu a yayin jawabin sa na ranar dimokuradiyya a ranar Laraba cewa an cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashi na kasa.