Kungiyar Jama’atul Nasrul Islam ta bukaci shugaba Buhari da ya dauki kwararan matakai domin kawo karshen kashe-kashen da ake yi a Najeriya

0 168

Kungiyar Jama’atul Nasrul Islam ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki kwararan matakai domin kawo karshen kashe-kashen da ake yi a kasarnan.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a jiya a wata sanarwa da sakatarenta Khalid Aliyu ya fitar.

Bayanin hakan na zuwa ne a matsayin martani kan kona matafiya da ba su ji ba ba su gani ba kwanannan da ‘yan bindiga suka yi a jihar Sakkwato.

Sanarwar ta Jama’atul Nasrul Islam ta zo ne a daidai lokacin da kungiyoyi da daidaikun jama’a a fadin kasarnan suke kira ga gwamnati da ta kawo karshen kashe-kashen da ake yi.

A rokonta ga shugaban kasa, kungiyar ta jawo ayoyin kur’ani mai tsarki da kuma kundin tsarin mulki, wadanda suka tabbatar da martabar ran Dan Adam.

Kungiyar ta kuma ce yadda ake ta kashe-kashen ba tare an dakile masu kisan ba, sannu a hankali Najeriya zata zama kasar da al’ummarta basa bin doka da oda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: