Kungiyar gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP sunyi alwashin kalubalantar matakin shugaban kasa na sanya dokar ta baci a jihar Rivers.
Idan dai z’a iya tinawa a jiya ne shugaban kasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihar Rivers wanda ya dakatar da gwamnan jihar Siminalayi Fubara, mataimakiyar sa da sauran zababbun yan majalisar dokoki a jihar.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa Hannun shugaban kungiyar, Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi, gwamoninin PDPn sun bukaci shugaban kasa ya amince ya aikata kuskure tare da warware matakin daya dauka.
Kungiyar ta kalubalanci shugaban kasa da nuna wariya, ta mai cewa ya fifita Ministan Abuja Nyeson Wike wanda ke kara rura wutar rikicin siyasar jihar a gwamnan.