Gwamnonin jihohin kasar nan 36 sun yanke shawarar ganawa da dukkan hukumomin tattalin arziki da na kudi domin tattauna batutuwan da suka shafi asusun tsaron jihohinsu.
Kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a Abdulrazak Bello-Barkindo, ya fitar jiya Lahadi a Abuja.
Bello-Barkindo ya ce za’a yi taron ne da nufin kawar da wasu matsaloli da suka dabaibaye asusun tsaron jihohinsu, wajen samar da ingantacciyar hanyar sarrafa kudaden.
Ya ce taron, bisa ga gayyatar da Darakta-Janar na kungoyar gwamnonin, Asishana Bayo Okauru ya bayar, zai gudana ta bidiyon kai tsaye, domin tabbatar da halartar dukkan jami’an da abin ya shafa a kan lamarin.
Ya lissafta wadanda aka gayyata zuwa taron da suka hada da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati, EFCC, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran laifuka masu alaka, ICPC, Hukumar tattara Haraji ta Kasa, da Babban Bankin kasa CBN.
Barkindo ya ce taron zai kuma yi la’akari da zurfafa gudanarwa da fadada manufofin karancin takardun kudi wanda aka soma tun shekarar 2022 lokacin da aka sake fasalin takardar Naira domin kara hada kan dukkan ‘yan kasa.
- Comments
- Facebook Comments