Kungiyar Fulani makiyaya tayi kira ga majalissar tarayya ta sanya baki kan matakin hana Fulani kiwo a a wasu jihohin Najeriya
Kungiyar Fulani makiyaya ta Kasa Miyetti Allah Kautal Hore, tayi kira ga majalissar tarayya ta sanya baki kan matakin da gwamnonin wasu jihohi a kasar nan suka dauka na hana Fulani kiwo a jihohinsu.
Sakataren kungiyar na kasa Malam Saleh Alhassan ne yayi wannan kiran, yayin wani taron bikin zaman lafiya na kasa da kuma karrama Sarauniya Amina da Temitope Ajayi a matsayin wakilan kungiyar Miyetti Allah da akai a karamar hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.
Alhassan yace dokar hana kiwon zata maida hannun agogo baya, a yakin da kasarnan keyi da matsalar satar shanu da, kwanciyar hankalin jama’ar karkara da sauransu
Bayaga koma baya ta fuskar samar da nama da madara, da dokar zata iya samarwa, Sakataren yace hana kiwon zai jefa miliyoyin jama’a cikin talauci da suka dogara kacokan kan kiyo a Najeriyar.
Daga nan, ya roki gwamnatin tarayya ta samar da ma’aikatar da zata lura da harkokin kiwon dabbobi da kifi a Najeriya kamar yadda ake dasu a sauran kasashen Nahiyar Afirka da dama