Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ta musanta zargin da ake yiwa kungiyar na kara farashin man zuwa naira 700 a fadin kasa.
Shugaban kungiyar na shiyyar Kudu maso Yamma Dele Tajudden ne ya musanta karin kudin man fetur din a zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN.
Shugaban kungiyar dillalan man fetur din ya bukaci al’umma dasu yi watsi da abinda ya kira jita-jitar da ke yawo kan karin kudin man. Ya ce farashin man fetur ba zai wuce yadda ake saida shi a yanzu ba.
Tajuddin ya godewa shugaban kasa bola tinubu bisa matakin cire tallafin man fetur, yace lamari ne da ya kamata a ce tuni an cire.
Ya kara da cewa karin farashin da aka samu akan kayayyaki na yau da kullum saboda tsadar sufuri, don haka ya kamata ‘yan Najeriya su hakuri domin kayayyakin ba za su kai ga talaka ba.
Ya yi nuni da cewa, an hana sayar da kayayyaki, don haka bambancin farashin ya faru ne ta hanyar sufuri saboda yana da alaka da wurin.