Kungiyar Amnesty ta nuna takaicin ta kan harin Bom da ya kashe sama da mutane 85 a Tudun Biri

0 238

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta nuna takaicin ta kan harin Bom bisa kuskure da ya kashe sama da mutane 85 a Kauyen Tudun Biri dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Kungiyar ta bayyana harin jirgin maras matuki da ya kashe fararen hula da abinda ba za’a laminta ba.

Kazalika, kungiyar ta soki dakarun sojin kasar nan sakamakon kai wannan hari, tare da neman a yi musu adalci da biyan diyya.

Amnesty tace dole gwamnatin shugaban kasa Tinubu ta dauki mataki kan wannan hari na jirgi maras matuki,ta hanyar gudanar da bincike domin tabbatar an hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan aikin.

Kungiyar ta Amnesty tace dole ayi adalci ga wadanda harin ya rutsa da su da iyalan su.

Ta kara da cewa tilas ne a kawo karshen harin jirgin sama maras matuki da ya ke sanadiyyar kashe fararen hula.

A watan Disembar shekarar 2022 harin jirgin saman maras matuki ya kashe mutane kimanin 64 a Kauyen Mutumji dake Jihar Zamfara.

Kazalika, a ranar 24 ga watan Janure na shekarar 2023 harin jirgin saman ya kashe makiyaya sama da 40 a yankin Doma na Jihar Nasarawa.

Sannan kuma a watan janerun wannan shekarar, wani harin jirgin saman na sojin kasar nan ya kashe gwamman mutane a garin Galadima Kogo na Jihar Neja. Daga shekarar 2021 kawo yanzu hare-hare jiragen sama sojin kasar nan ya kashe fararen hula kimanin 115.

Leave a Reply

%d bloggers like this: