Kungiyar ADSI ta bukaci shugaba Tinubu da ya tunkari matsalar ilimin yara musamman a yankin arewacin Najeriya

0 316

Kungiyar masu fafutukar goyon bayan cigaban Arewa (ADSI), ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tunkari matsalar ilimin yara mata da yara da ba sa zuwa makaranta, musamman a yankin arewacin kasar nan.

Shugaban kungiyar, Khuraira Musa, a cikin wata sanarwa da ta fitar domin bikin Eid-el Kabir, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da mafita mai ɗorewa kan rikicin manoma da makiyaya a ƙasar.

ADSI ta jaddada bukatar gwamnatin tarayya ta kawo manoma da makiyaya a kan teburin tattaunawa domin tunkarar lamarin. Kungiyar ta kuma bayyana kudurin ta na hada kai da gwamnati domin sake gina yankin arewa da kuma Najeriya baki daya ta hanyar koyon sana’o’i da ilimi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: