Kudirin gwamnatina ta bangaren kwallon kafa don ci gaban ‘ya’ya mata ne da matasa – Buhari

0 134

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kudirin gwamnatinsa na amfani da kwallon kafa don ci gaban ‘ya’ya mata, tare da zaburar da matasa don samun ayyukan yi masu kyau a wasannin.

Shugaban kasar ya yi magana a yau yayin karbar bakuncin tawagar FIFA karkashin jagorancin shugaban ta, Gianni Infantino, da shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF), Patrice Motsepe, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ya yi kira ga babbar hukumar kwallon kafa ta duniya da ta dauki Najeriya a matsayin daya daga cikin manyan kasashe idan aka zo batun ci gaban kwallon kafa.

Game da kwallon kafa ta mata, Shugaban kasar ya nuna farin cikinsa cewa Najeriya ta samar da kyawawan ababen koyi don zaburar da taurari masu sha’awar shiga wasannin.

Shugaban kasar, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Femi Adesina ya fitar, ya shaida wa shugaban FIFA da ke ziyara cewa tun daga shekarar 2017, gwamnatinsa ta dauki kwallon kafa da muhimmancin gaske.

Leave a Reply

%d bloggers like this: