Kotuna a garin Kafin hausa sun zartar da hukuncin daurin watanni 3 ga wasu maza da mata guda 40

0 175

Manyan kotunan shariar musulunci na garin Kafin hausa sun zartar da hukuncin daurin watanni uku ko kuma zabin biyan tarar naira dubu 10-10 ga wasu maza da mata guda 40 da aka samu da aikata lefuka daban-daban da suka sabawa sashe na 374  da kuma na 20 na dokar panel code ta jihar Jigawa

Alkalan kotunan Aliyu Muhammad da kuma Inuwa Sa’idu Dabo suka bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala zartar da hukuncin.

Alkalan Mallam Aliyu da kuma Inuwa Dabo sun ce kwamitin karta kwana da karamar hukumar ta kafa domin yaki da masu aikata lefuka ne suka kama masu lefin a kauyen Tage.

Masu lefin sun sanya hannu akan yarjejeniyar cewar ba zasu sake aikata irin wannan lefin ba tare da alkawarin kaurewar aikata irin wadannan lefuka.

A jawabinsa shugaban kwamitin kuma kwamandan Hisba na yankin Abdulkadir Zakar ya yi godiya ga Allah da a suka sami nasarar kamawa da kuma hukunta masu aikata lefuka a yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: