Kotun ta bada umarnin sakin hambarar shugaban kasar Nijar Muhammad Bazoum

0 323

Kotun ECOWAS a jiya Juma’a ta bada umarnin sakin hambarar shugaban kasar Nijar Muhammad Bazoum, wanda sojojin da suka yi juyin mulki ke tsare da shi tun ranar 26 ga watan Yuli.

Yayin zaman kotun na jiya Juma’a a Abuja babban Birnin kasar nan, kotun tace ya zama wajibi a saki hambarar shugaban kasar ta Nijar Mohammad Bazoum.

Nijar na fuskantar takunkumi daga kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta yamma ECOWAS tun bayan da sojojin dake tsaren shugaban kasar suka hambarar da shi tare da tsare shi da iyalansa.

Bazaoum tare da matarsa da Dansa na zaune a fadar shugaban kasar Nijar tun lokacin da sojojin kasar suka yi masa juyin mulki. Har yanzu dai sojojin dake jan ragamar shugabancin kasar ba su ce komai ba dangane da wannan umarnin kotun.

Leave a Reply

%d bloggers like this: