Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman, tare da ba da umarnin sake zabe a rumfunan zabe biyar.
Kotun mai Alkalai uku karkashin jagorancin mai shari’a O.O Adejumo sun yi watsi da karar da shugaban majalisar ya shigar tare da bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe biyar maimakon 42 da kotun ta bayar.
A ranar 30 ga watan Satumba ne kotun sauraren kararrakin zabe ta majalisar dokokin jihar Kaduna ta soke nasarar da Liman ya samu wanda ke wakiltar mazabar Makera tare da ba da umarnin sake zabe a rumfunan zabe 42.
Hakan ya biyo bayan karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Solomon Katuka, ya shigar gaban kotun yana kalubalantar zaben Liman na jam’iyyar APC.
A cikin karar da ya shigar, dan takarar na PDP ya yi zargin cewa an tabka kura-kurai game da zaben shugaban majalisar, inda ya ce a gaskiya shi ne ya lashe zaben majalisar dokokin da aka gudanar a mazabar Makera a ranar 18 ga Maris, don haka ya kamata a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben. A hukuncin kotun daukaka kara, APC na da kuri’u dubu 17 da dari 470 yayin da PDP ta samu kuri’u dubu 17 da 88.