Kotun daukaka kara da ke zamanta a garin Fatakwal na jihar Ribas ta janye sammacin kamu da wata babbar kotun jihar Ribas ta bayar a kan karar da gwamnatin jihar ta shigar kan tsohon gwamnan jihar, Chibuike Rotimi Amaechi da wasu mutane biyar. Amaechi ya kasance tsohon ministan sufuri a gwamnatin Muhammadu Buhari.
Mai shari’a Chiwendu Nwogu na babbar kotun jihar Ribas a ranar 17 ga Mayu, 2023, ya bayar da sammacin kama Amaechi da kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar (APC) a jihar, Tonye Cole, tsohon kwamishinan makamashi, Augustine. Wokocha da wasu uku da aka kalubalanta a kotun daukaka kara.
Kwamitin mai mutum uku karkashin jagorancin mai shari’a Joseph Ikyegh, a cikin hukuncin daya yanke kan bukatar, ya ce babbar kotun jihar Ribas ba daidai ba ne ta ci gaba da shari’ar a lokacin da tuni ake kalubalantar matakin a kotun daukaka kara.
An rawaiito cewa kwamitin mai mutum uku na kotun daukaka kara ya kuma yi watsi da umarnin kama Amaechi da wasu mutane 5 tare da yin la’akari da yadda ake aiwatar da aikin a kan wadanda ake kara.