Babbar kotun babban birnin tarayya da ke Abuja ta yankewa wasu masu damfarar yanar gizo su 10 hukunci.
Wata sanarwa da Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta fitar a jiya, ta ce alkalin kotun, Hamza Mu’azu, ya yanke wa masu laifin hukuncin daurin shekaru daban-daban tare da zabin biyan tara a ranar Alhamis.
A cewar mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, hukuncin da aka yankewa mutanen ya kasance tsakanin watanni 3 zuwa 6 tare da zabin biyan tarar naira dubu 20 zuwa dubu 100.
Wadanda aka yankewa hukuncin sune: Ulukpo Victor Obokparo, Osondu Stanley, Habib Iko-Ojo, Precious Ani, Emmanuel Philip Ikpan, Umar Farouk Mohammed, Israel Kue, Kingsley Mathew, Ibrahim Oyolade da Taiwo Samuel.
An same su da laifin yaudara, zamba ta soyayya, samun kudade ta hanyar cuta da yaudarar ‘yan kasashen waje ta hanyar intanet.