Kotu ta yanke wa wani hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe abokinsa akan kudi ₦100

0 517

Babbar kotun jihar Zamfara ta yanke wa wani mai suna Anas Dahiru hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe abokinsa kan kudi naira 100.

An gurfanar da Dahiru kotu ne a watan Yunin 2017 bisa zarginsa da kashe abokinsa, mai suna Shamu Ibrahim, ta hanyar cika masa wuka a lokacin da suke fada da juna kan kudi Naira 100.

Da yake karanta hukuncin, alkalin kotun, Mai shari’a Mukhtar Yusha’u, ya ce wanda ake zargin Anas Dahiru dake Unguwar Dallatu a Gusau babban birnin jihar, an gurfanar da shi a gaban kotu a shekarar 2017 bisa zargin kashe abokinsa, Shamsu Ibrahim, da wuka akan rigimar kudi naira 100 kacal.

Yusha’u ya ce kotun ta saurari bangarorin biyu bayan haka ne kotun ta sami Anas da laifin kashe abokinsa.

A wani labarin kuma, alkalin kotun ya kuma yankewa wani mai suna Sadiku Abubakar hukunci bisa laifin yunkurin yin fashi da makami a karamar hukumar Bungudu.

An yankewa Sadiqu hukuncin ne bayan yunkurin yiwa wani dan kasuwa a kauyen Runji dake karamar hukumar Bungudu fashi da makami inda daga bisani aka damke dan fashin tare da mika shi ga ‘yan sanda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: