Wata kotun sauraron kararkin zaɓe da ke zaune a birnin Lokoja a jihar Kogi ta soke zaɓen sanatan Kogi ta Yamma Dino Melaye.
A lokacin da ya ke yankin hukuncin alƙalin kotun ya bayar da umarnin a sake sabon zaɓe a mazabar ta Kogi ta Yamma ba tare da ɓata lokaci ba
Sai dai a wani sabon bidiyo da ya fitar a shafinsa na Facebook Dino ya ce wannan hukuncin ba zai dauke masa hankali ba, kuma tuni sun bi matakan daukaka kara.