Kotu ta bayyana Simon Lalong a matsayin wanda ya lashe zaɓen kujerar majalisar dattawa mai wakiltar Filato ta kudu

0 248

Kotun sauraren ƙararrakin zaɓen ‘yan majalisar dattawa ta kasa, mai mazanta a Jos da ke jihar Filato, ta bayyana tsohon gwamnan jihar Simon Lalong wanda ya tsaya takarar ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Filato ta kudu a ƙarkashin jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Alƙalin da ya jagoranci bayyana hukuncin, Mai shari’a Mahmoud Tukur, ya yanke hukunci cewa yawan ƙuri’un da ɗan takarar jam’iyyar PDP, Napoleon Bali ya samu sun tafi a banza, saboda an zaɓe shi ba bisa ƙa’ida ba.

Hukuncin wanda aka yanke a ranar Litinin da kuma ya samu goyon bayan dukkan alƙalan, ya bayyana cewa a lokacin da aka gudanar da zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 jam’iyyar PDP ba ta da cikakken shugabanci a jihar, kazalika sun yi watsi da batun da ya shafi zargin yin aringizon ƙuri’u inda suka ce babu gamsassun hujjoji da za su tabbatar da hakan.

Haka ma jam’iyyar PDP ta rasa kujerar ɗan majalisar wakiai mai wakiltar mazaɓun tarayya na Barikin Ladi da Riyom inda aka tabbatar da Dalyop Chollom na jam’iyyar LP a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Kotun ta yanke hukuncin cewa Peter Gyenden na jam’iyyar PDP ba shi ne zaɓaɓɓen Sanatan ba sakamakon jam’iyyarsa ba ta da cikakken shugabanci a jihar ta Filato a lokacin da aka gudanar da zaɓukan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: