Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, babban birnin Najeriya ta ɗage sauraron shari’ar da ake yi wa shugaban ƙungiyar masu rajin kafa ƙasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu.
Ana tuhumar Kanu da laifuka da dama, waɗanda suka jiɓanci ta’addanci, tun bayan kama shi da kuma mayar da shi Najeriya a watan Yunin 2021.
Tun a wancan lokacin ake ci gaba da tsare jagoran na IPOB, kuma duk wani yunƙuri na neman beli ya ci tura.
A baya an samu tsaiko wajen ci gaba da shari’ar bayan da Mista Kanu ya buƙaci mai sauraron ƙarar, Binta Nyako ta tsame kanta daga shari’ar kasancewar “ba ya da ƙwarin gwiwa a kan ta.”
Nyako ta sanar cewa ta tsame kanta daga shari’ar. To sai dai babban alƙalin kotun ya sake mayar wa alƙaliyar takardun shari’ar domin ta ci gaba da jan ragamarta, kasancewar Nnamdi Kanu bai gabatar da buƙatar tasa a rubuce ba.
A zaman na yau Litini, mai shari’a Binta Nyako ta ce babban alƙalin kotun bai amince da janyewar tata ba.
Ta kuma buƙaci masu kare Kanu da su gabatar da buƙatarsu a rubuce, matuƙar suna nan a kan bakarsu ta cewa sai ta tsame kanta daga shari’ar.