Kotu na zama kan shari’ar Najeriya da kamfanin mai na Shell a Landan

0 132

Yau ne wata babbar kotu a birnin Landan na Birtaniya ke zaman sauraron ƙorafin farko-farko a ƙarar da Najeriya ta shigar da kamfanin haƙar man fetur na Shell kan malalar ɗanyen man fetur a yankin Neja-Delta.

Ana sa ran lauyoyin da ke tsaya wa Najeriya za su buƙaci kamfanin Shell ya amsa laifin illar da gurɓacewar muhallin da kwararar mai ya haifar tsakanin shekarun 1989 zuwa 2020.

Hukumomin Najeriya sun ce wannan lamari ya yi tarnaƙi ga samar da ruwan sha mai tsafta ga al’ummar yankin, da lalata gonaki da hana ayyukan kamun kifi, tare da zama barazana ga lafiyar al’umma.

Kamfanin na Shell dai ya musanta aikata ba daidai ba.

Kuma ya ɗora alhakin malalar man a yankin Ogoni kan ayyukan masu satar ɗanyen mai da kuma wuraren tace man ba bisa ka’ida ba.

Leave a Reply