Wata kotu a Senegal ta yanke hukuncin daurin talala na watanni shida da cin tarar dala dubu 300 ga wani babban dan siyasar adawa, Ousmane Sonko, wanda ke da niyyar tsayawa takara a zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa.
Ousmane Sonko, wanda aka samu da laifin bata sunan ministan yawon bude ido na kasar, ya samu hukuncin daurin talala na watanni biyu a watan Maris.
Amma mai gabatar da kara ya bukaci a kara yawan watannin bayan an daukaka kara.
Ousmane Sonko dai bai gurfana a gaban kotun ba a jiya domin sauraron karar sannan kuma ya bayyana cewa ba zai sake amsa sammacin da kotu ta yi masa ba har sai an tabbatar da tsaron lafiyarsa.
Masu aiko da rahotanni sun ce ‘yan adawa na kallon daukacin shari’ar a matsayin wani yunkuri na tabbatar da Ousmane Sonko ba zai iya tsayawa takarar shugaban kasa ba.
Shugaban kasa mai ci Macky Sall na iya sake neman wa’adi na uku duk da kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade wa’adi 2.