Kotu A Jihar Ondo Ta Samu Kararraki Biyu Kan Zaben Majalisar Dokokin Jihar

0 142

Kotun sauraren kararrakin zabe a jihar Ondo ta ce ta samu kararraki biyu kan zaben majalisar dokokin jihar da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Sakataren kotun, Malam Musa Adam, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na kasa a Akure ranar Juma’a cewa koke-koke biyu sun fito ne daga ‘yan takarar jam’iyyar PDP a kan ‘yan takarar jam’iyyar APC.
Adam ya bayyana cewa dan takarar PDP na mazabar Aderemi Oyewole, ya kai karar dan takarar jam’iyyar APC na mazabar Mrs Tosin Ogunlowo da hukumar zabe mai zaman kanta da kuma jam’iyyar APC.
Ya kara da cewa, Babatunde Fadare, dan takarar PDP a mazabar Ile-Oluji/Oke-Igbo, ya kai karar dan takarar APC a mazabar, Mista Nelson Akinsuroju, hukumar zabe mai zaman kanta da kuma jam’iyyar APC.
Sakataren ya ce bisa tanadin dokar zabe, duk dan takarar da bai gamsu ba yana da wa’adin kwanaki 21 daga ranar zabe domin gabatar da koke domin kalubalantar sakamakon zaben.
Adam ya bayyana cewa da zarar an shigar da kara, doka ta tanadi kwanaki 180 ko watanni shida kafin a kammala ta kuma a tantance.
NAN ta ruwaito cewa a baya kotun ta karbi kararraki tara kan zaben ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar inda masu shigar da kara suka janye kararraki guda biyu, saura bakwai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: