Ko Kunsan An Yi Yunkurin Juyin Mulki A Jamhuriyar Nijar?

0 174

An yi yunkurin juyin mulki a jamhuriyar Nijar a yayin da ake gab da mika jagorancin kasar ga Shugaba mai jiran gado Mohamed Bazoum.

Mazauna birnin Niamey na kasar sun tabbatar da jin rugugin harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Kasar da ke birnin tun da misalin karfe 3 na Asubahin ranar Laraba.

Wasu kafafen yada labarai na kasashen sun ruwaito cewa ana yunkurin yin juyin mulki ne a kasar, da ta tsinci kanta a cikin rikicin siyasa tun bayan ayyana Bazoum a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasar na watan Fabrairu.

Gidan talabijin na France24 mallakin kasar Faransa wadda ta mulki Jamhuriyar Nijar ya ce dakarun gwamnatin Kasar sun yi nasarar dakile yunkurin juyin mulkin.

Rahotannin sun ce ofisoshin jakadancin kasashen waje da ke birnin sun bukaci ma’aikatansu da su zauna a gida tukuna.

Har yanzu babu tabbacin musabbabin harbe-harben a hukumance, amma dai gidan rediyon gwamnatin kasar da ke Niamey din ya ci gaba da gabatar da shirye-shiryensa kamar yadda ya saba.

Wasu majiyoyi kuma sun bayyana cewa yanzu da alama lamarin ya dan lafa.

Kasar Nijar na fama da hare-haren ’yan bindiga kamar sauran makwabtanta na yankin Sahel, inda kungiyar Boko Haram da kungiyar ISWAP da dangoginsu suke addaba.

Bayan zaben Bazoum wanda shi ne tsohon Ministan Harkokin Kasashen Waje, abokin karawarsa kuma tshon Shubagan Kasar, Mahamane Ousmane, wanda aka kayar a zagaye na biyu ya yi watsi da sakamakon bisa zargin an yi magudi.

A makon jiha Kotun Kolin kasar ta tabbatar da nasarar Bazoum, wanda shi ne dan lelen Shugaba Mahamadou Issoufou mai barin gado, wanda kuma zai kai ga rantsar da Bazoum din a matsayin Shugaban Kasa a ranar Juma’a, 2 ga Afilu.

Bikin na ranar Juma’a sh ine zai zama karon farko da aka mika mulki tsakanin zababbun gwamnatocin dimokuradiyya a tarihin kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: