Kimanin yara dubu 459 da 959 ake sa ran yiwa rigakafin cutar shan inna a karamar hukumar Hadejia a yayin aikin rigakafin.
Da yake jawabi, Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Abdulkadir Bala Umar T.O ya umarci ma’aikatan rigakafin da su tabbatar da cewa an yiwa dukkan yaran da suka cancanta ayi musu.
Shugaban ya kuma bukaci iyaye da su bayar da hadin kai ta hanyar fito da yaransu domin rigakafin.
Ya ce ana kashe makudan kudade don tabbatar da yara sun kubuta daga muguwar cutar.
A nasa jawabin Manajan kula da lafiya matakin farko na karamar hukumar Alhaji Idris Wuriwa ya ce an dauki ma’aikatan wucin gadi 260 domin samun nasarar gudanar da aikin yayin da aka samar da isassun alluran rigakafi daga gwamnatin jiha.
Ya kara da cewa Majalisar Karamar Hukumar ta tallafawa aikin ta hanyar samar da katan 35 na alewa da za a bai wa kowane yaro da aka yi wa rigakafin a yankin.