Katsina: Kimanin Gonakai dubu 50,000 aka daina Nomawa saboda yan bindiga

0 150

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa kimanin Gonakai KadadaN Noma dubu 50,000 ne aka daina Nomawa a shekarar 2020, saboda hare-haren yan Bindiga.

Gwamna Masari ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da Noman Masara na shekarar 2021 da kuma kaddamar da Dalar Masara wanda ita ce ta farko da aka fara gudanarwa a Najeriya.

Kungiyar Masu Noman Masara ta Kasa tare da hadin Gwiwar Babban Bankin Kasa CBN sune suka shirya taron.

A cewar Gwamna Masari duk da hare-haren yan bindigar, Manoma sun samu Yabanya mai kyau.

Gwamna Masari ya ce shirin bawa manoma ranche ya tallafawa wajen inganta rayuwar kananan Manoma a Jihar.

Kazalika, ya ce cikin shekaru 5 da suka gabata, Jihar tayi nasarar Samawa Matasa Miliyan 1 da dubu 200 aikin wucin gadi, tare da samawa Matasa dubu 249,551 ayyukanyi na watanni 6 zuwa Sama.

A jawabinsa Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir, wanda Lawan Bagiwa, ya wakilta ya yabawa bankin CBN da Kungiyar Masu Noma Marasa bisa nasarar da suka samu a shirin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: