Kashim Shettima ya ziyarci IBB da Abdulsalami Abubakar.

0 194

mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, jiya ya ziyarci tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida da tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar.

Shettima wanda ke Minna, babban birnin jihar Neja, ya yi ziyara ta musamman  ga tsaffin shugabannin Najeriya biyu a cikin watan Ramadan.

Majiyoyin da suka fito da ga shugabannin biyu sun shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ziyarar da Shettima ya kai ba ta rasa nasaba da gwamnatin APC mai zuwa da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu zai jagoranta.

Majiyar ta ce Tinubu na neman goyon bayan manyan shugabannin biyu. An kuma tattaro cewa matakin da mataimakin shugaban kasar ya dauka na tuntubar tsoffin shugabannin sojoji biyu ne kan shirin da wasu ‘yan siyasa ke yi na kafa gwamnatin wucin gadi kamar yadda hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta tabbatar a ranar Laraba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: