Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya ƙadammar da shirin gina rukunin gidaje da makarantu da asibitoci da aka yi wa laƙabi da Pulako a garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna. Yanki ne da sojojin ƙasar suka kai wa hari ta sama bisa kuskure a bara, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.