Jamus ta sanar da gudunmawar kudi euro miliyan 26, kwatankwacin Naira Biliyan 11 da miliyan 325 da dubu 630 da 732, domin agazawa Najeriya a yakin da take da cutar corona.
Ofishin jakadancin Jamus a Najeriya cikin wata sanarwa yace an bayar da gudunmawar domin nuna goyon baya da hadin kai ga Najeriya a lokacin annobar.
Sanarwar ta yi nuni da cewa kudaden zasu samar da ayyukan agaji a Arewa Maso Gabas, musamman a jihoshin Borno da Yobe da Adamawa.
- Gwamnatin tarayya na shirin bunkasa tattalin arzikin Najeriya zuwa darajar dala tiriliyan daya
- Natasha ta bawa Sanata Akpabio hakuri cikin wasika mai cike da zolaya
- Mai Mala Buni ya yi watsi da rahotannin cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar APC
- ‘Yan siyasa na rikici da juna ne don samun mukamai ba dan jin dadin jama’a ba – Attahiru Bafarawa
- Watan Zul’kida bai kama ba a Najeriya – Fadar Sarkin Musulmi
Sanarwar ta yi bayanin cewa gwamnatin Jamus tana samar da tallafin kudade domin ayyukan agaji a Arewa maso Gabas na Najeriya da yankunan kan iyaka na Chadi da Nijar da Kamaru.
Ofishin jakadancin yayi bayanin cewa euro miliyan 8 zai tafi zuwa shirin abinci na majalisar dinkin duniya a Najeriya, euro miliyan 7 zai tafi zuwa kwamitin kasa da kasa na Red Cross a Najeriya, yayin da euro miliyan 5 zai je ga hukumar abinci da aikin gona ta majalisar dinkin duniya a Najeriya, da sauransu.