Kasar Isra’ila ta kashe shugaban Hamas a Lebanon
Ƙungiyar Hamas ta Zirin Gaza ta sanar da cewa an kashe shugabanta a Lebanon, Fateh Sherif Abu el-Amin, tare da wasu ‘yan’uwansa sakamakon harin Isra’ila a kudancin Lebanon.
Hamas ta ce harin ya faɗa kan gidansa da ke sansanin Al-Bass.
Tun da farko kamfanin labarai na gwamnatin Lebanon ya ruwaito harin a kusa da garin Tyre.
Duk da cewa Hamas a Gaza take al’amuranta – inda Isra’ila ke kai hare-hare tun ranar 7 ga watan Oktoba – tana kuma gudanar da ayyuka a Lebanon.
Iran ce ke taimaka wa Hezbollah da Hamas.
- BBC