Kasar Gabon ta samu la’adar kudi saboda kokarinta na yaki da saran dazuka da rage fitar da gurbatacciyar iska

0 205

Kasar Gabon ta zama kasar Afirka ta farko da aka biya ta ladar kudi saboda kokarinta na yaki da saran dazuka da rage fitar da gurbatacciyar iska.

Ministan muhalli na kasar ya ce za a fara biyan farko na dala miliyan 17 wajen kare dazukan da suka mamaye kusan kashi 90 na kasar.

A cikin shekaru 10 masu zuwa, gwamnatin kasar Gabon za ta karbi jimillar kudi dala miliyan 150 daga shirin Majalisar Dinkin Duniya na kula da dazukan Afirka ta Tsakiya.

Kasar ta kaddamar da wasu tsarin kiyaye muhalli a shekarun da suka gabata, ciki har da kirkiro wuraren shakatawa guda 13 da kuma wani shirin yaki da sare bishiyoyi ba bisa ka’ida ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: